Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa; jabahatul Islama a kasar Jodan ce ta yi nuni da hare-hare da munanan shirye-shirye na zagon kasa da gwamnatin haramtacciyar kasar ke yi wa masallacin a makircin ruguza shi . Wannan inji wannan kungiya ya bayyana hakikani da mummunan hadarin da masallacin ke fuskanta . Komitin kula da masallacin a fadar sarkin jodan ya bukaci hana wannan hari da Yahudawan sahayoniya ke kai wa masallacin da kuma bukatar kungiyar kasashen musulmi da ta dauki matakin gaggawa kan wanna lamari.
394674