Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alra'ayi cewa; babban daraktan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Kuwait ya bayyana cewawa'adin da aka bayar na rijistar sunayen wadanda za su shiga gasar kur'ani a kasar na gab da kawo karshe. Muhammad Abdullah Aljalahimah ya bayyana cewa bangaren da ke kula karatun kur'ani gami da gasar da ake shiryawa shi ne zai dauki nauyin shirya wanna gasa ta kasa baki daya, ya ce wadanda suke niyar shiga gasar kuma bas u samu sun yi rijista har yanzu, su gaggauta yin rijistar kafin karewar wa'adin. Ya kara da cewa babbar manufar gudanar da gasar dai ita ce karfafa gwiwar matasa wajen harda da kuma karatun kur'ani.
396036