Bnagaren kasa da kasa: An buga tare da yada wani littafi a hukumance kan hakikanin manufofin addinin musulunci tare da hannuka mai sanda muslunci ke yi a cikin rayuwar dan adam.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Islamonline cewa; An buga tare da yada wani littafi a hukumance kan hakikanin manufofin addinin musulunci tare da hannuka mai sanda muslunci ke yi a cikin rayuwar dan adam. Bayanin ya ci gaba da cewa ma'aikatar kula harkokin 'yan gudun hijira ta kasar ce ta dauki nauyin buga littafin, domin sauran al'ummomin kasar su kara samun natsuwa dangane da muslunci maimakon tsanarsa da wasu ke yi, bisa la'akari da yawan da musulmi suke karawa a kasar, da kuma kara yawaitar masallatai da cibiyoyin addinin musulunci. Yanzu haka dai musulmi da yawansu ya kai miliyan daya da dubu dari uku a kasar Spain, inda birnin Catalonia yake da musulmi sama da dubu dari uku.
396009