IQNA

20:32 - April 30, 2009
Lambar Labari: 1772076

An Tattauna Kan 'Yancin Bin Mazhaba A Mahangar Fikihun Musulunci

Bangaren kasa da kasa: Kimanin malamai 250 gami dam asana daga daga kasashen muslmi daban-daban ne suke ci gaba da gudanar da taron cibiyar fikihun muslunci a karo na 19 a birnin Shatjan na Hadaddiyar Daular Larabawa, inda suka tattauna batun 'yancin bin mazhaba da kuma 'yan bayyana ra'ayi gami da hukuncin ridda.

Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jarodar Almadina da ake bugawa a kasar saudiyya cewa; Kimanin malamai 250 gami dam asana daga daga kasashen muslmi daban-daban ne suke ci gaba da gudanar da taron cibiyar fikihun muslunci a karo na 19 a birnin Shatjan na Hadaddiyar Daular Larabawa, inda suka tattauna batun 'yancin bin mazhaba da kuma 'yan bayyana ra'ayi gami da hukuncin ridda. Yau ne taron ya shiga rana ta biyu, inda mahalarta taron ke gaba da tattauna muhimman batutuwa da suke ci ma duniyar musulunci tuwo a kwarya, gami da muhimman batutuwa da suke da dangantaka da fikihun musulunci, wanda kuma haduwar malamai da suka fito daga mabanbantan mazhabobi da haduwarsu kan kan lamari guda hakan ne kawai babbar hanyar warware irin wadannan matsaloli.


396832
captcha