Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: kamfanin dillancin labaran gwamnatin Saudiya Spa ta watsa rahoton cewa: wannan taro na kwana daya hadin guiwar kungiyoyin musulmai na duniya tare da hadin guiwar kungiyar musulmin Benin suka shirya . Har ila yau a wannan taro akwai halartar malumman masallatai da shugabannin kungiyoyin musulunci a kasar ta Benin da kuma na sauran kasashen musulmi na Afrika da na duniya baki daya.
398056