IQNA

An Fara Gudanar Taron Palastinawa Na Kasa Da Kasa A Italia

15:11 - May 04, 2009
Lambar Labari: 1773874
Bangaren kasa da kasa: an fara gudanar da taron palastinawa mazauna nahiyar turai a kasar Italia, mai taken jaddada hakkin dawowar palastinawa zuwa zuwa kasarsu Palastinu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Muslim cewa; : an fara gudanar da taron palastinawa mazauna nahiyar turai a kasar Italia, mai taken jaddada hakkin dawowar palastinawa zuwa zuwa kasarsu Palastinu. Taron wanda ke samun halartar palastinawa mazauna kasashe daban-daban na nahiyar turai, da ake gudanarwa a kasar Italia, ya mayar da hankali ne kan batun hakkin dukkanin al'ummar palastinu da a halin yanzu ahaka suke gudun hijira a kasashen duniya daban-daban su koma gida, tare da yi kira ga dukkanin bangarori na kasa da kasa da su safke nauyin da ya rataya kansu na takawa Isra'ila birki kan tabargazar da take tafkawa kan alummar palastinu marassa kariya, tare da gudanar da sahihin bincike kan ayyukan ta'addancin da ta aikata kan al'ummar Gaza a 'yan watanni da suka gabata.


398326
captcha