IQNA

Yaki Da Nuna wariya Wani Bangare Ne Na Addinin Musulunci

15:24 - May 05, 2009
Lambar Labari: 1774360
Bangaren kasa da kasa: Duniyar musulunci tana da wasu amuhimman abubuwa da ta kebanta da su tun tsawon tarihi, wadannan abubuwa kuwa sun hada da yaki da nuna wariyar al'umma ko launin fata, tare da bayar da damar bayyana ra'ayi da akida tare da kare hakkin dan adam da na mabiya addinai daban-daban gami da al'adun al'ummomi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Albayan da ake bugawa a kasar hadaddiyar daular larabawa cewa; shugaban kwamitin masallacin ma'aiki da ke birnin madina mai alfarma Saleh Abdulrahman Hasin ya bayyana cewa; Duniyar musulunci tana da wasu amuhimman abubuwa da ta kebanta da su tun tsawon tarihi, wadannan abubuwa kuwa sun hada da yaki da nuna wariyar al'umma ko launin fata, tare da bayar da damar bayyana ra'ayi da akida tare da kare hakkin dan adam da na mabiya addinai daban-daban gami da al'adun al'ummomi. Ya ci gaba da cewa addinin musulunci tun farko addini ne ana rangwanta ma juna tare da sulhu da zaman lafiya tsakaninsa da sauran addinai, masu kokarin bayyana addinin musulunci a matasayin addini tashin hankali a kasashen turai suna yin kuskure ne.

399443

captcha