Bangaren kasa da kasa: Wasu daga cikin masana da kuma 'yan siyasar kasar Masar sun fitar da wani bayani a jiya, da a cikinsa suka bayyana cewa siyasar da Isra'ila take gudanarwa a birnin Qods siyasa ce ta nuna wariya ga palastinawa, da yunkurin mayar da birnin na yahudawa tare da share duk wasu alamu na musulunci da ke birnin.
Kamafanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na arabonline cewa; Wasu daga cikin masana da kuma 'yan siyasar kasar Masar sun fitar da wani bayani a jiya, da a cikinsa suka bayyana cewa siyasar da Isra'ila take gudanarwa a birnin Qods siyasa ce ta nuna wariya ga palastinawa, da yunkurin mayar da birnin na yahudawa tare da share duk wasu alamu na musulunci da ke birnin. Bayanin ya ci gaba da cewa wajibi ne da ya rataya kan kasashen muslumi a matsayi na al'umma da kuma gwamnatoci da su kare alfarmar birnin Qods da wurare masu tsarki da ke cikinsa, da a halin yanzu ke fuskantar baraza daga yahudawan sahyuniya masu tsattsauran ra'ayi da suka kafa gwamnati a Isra'ila. Ba'ada bayan haka kuma wajibi ne kan al'ummomin musulmi da na larabawa da su kare 'yan uwansu palastinawa da ke fuskantar barazana daga yahudawan sahyuniya a Qods da sauran yankunan palastinu.
401622