Bangaren kur'ani: Wani fitaccen makarancin kur'ani dan kasar Iran Amin Puya ya bayyana cewa yawan tilawa da kuma dawwama a kanta na taimaka ma makaranta kur'ani a lokacin gasa, tare da kiyaye ka'idojin da ake bukatar kiyayewa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Wani fitaccen makarancin kur'ani ya bayyana cewa yawan tilawa da kuma dawwama a kanta na taimaka ma makaranta kur'ani a lokacin gasa, tare da kiyaye ka'idojin da ake bukatar kiyayewa. Makarancin ya bayyana hank ne a wani zama na mako-mako, inda yake koyar da karatun kur'ani mai tsarki da hakan ya hada da karatu gami da harda ga masu sha'awa. Ya kara da cewa dole ne mu yi koyi da kyawawan abubuwa domin mu samu kyakkyawan sakamako a cikin dukkanin lamurranmu, a kan haka abin da ya shafi karatun kur'ani dole ne makaranci ya lizimci yin tilawa, domin hakan ne zai taimaka masa wajen tabbatar da harda ko karatunsa.
402103