Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; Hujjatul Islam da musulmi Abdul Amir Kablan mataimakin shugaban komitin islama nay an shi'a a kasar Labanon a wata ganawa da ya yi da Muhammad Huseini Ra'is Zade mai kula da ofishin yada al'adun Iran a kasar ta Labanon da kuma wata tawaga ta malumai da masana masu bincike a a cibiyar Imam Khomeini ® ya yi bayanin cewa: a yau yan shi'a na fadi tashin ganin sun yada addinin Musulunci ta hanya madaidaiciya ta hakika a fadin duniya musamman a yammacin Turai inda ake yi masa mummunan kallo da fassara.
402721