Bangaren kasa da kasa: Jaridar Post Club da ake bugawa a kasar Amurka ta nakalto daga jagoran mabiya addinin buda Dalai lama cewa ana gurbata ma'anar jihadi a mahangar addinin musulunci a duniya, ta yadda ake bayyana ma'anar ba yadda musulunci ke nufi ba.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na islam online cewa; Jaridar Post Club da ake bugawa a kasar Amurka ta nakalto daga jagoran mabiya addinin buda Dalai lama cewa ana gurbata ma'anar jihadi a mahangar addinin musulunci a duniya, ta yadda ake bayyana ma'anar ba yadda musulunci ke nufi ba. Dalai lama ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban dubban daliban jami'ar Haward, ya ci gaba da cewa duk wanda ya san ma'anar jihadi a addinin musulunci zai fahimci cewa jihadin musulunci ba shi da wata manufa ta cutarwa, illa manufa ta kare kai kawai, amma abin takaici shi ne yadda aka wayi gari an canja wannan ma'ana tare da yada wata maa'anar ta daban da sunan addinin musulunci. Ya ce ma'anar kalma Allah ba wata aba ce ba illa so da kauna, wadda kuma ita ce musulmi da wanda ba musulmi ba suka yi ammana da ita.
403367