IQNA

An Baje Kolin Kayan Tarihi Da Suka Danganci Kur'ani A Senegal

15:20 - May 12, 2009
Lambar Labari: 1777499
Bangaren kasa da kasa: An baje kolin kayayyakin tarihi da suka danganci kur'ani a birnin Thies na kasar Senegal, a lokacin da ake baje kolin kayyakin tarihi na kasar a wannan birnin.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran walf sn cewa; An baje kolin kayayyakin tarihi da suka danganci kur'ani a birnin Thies na kasar Senegal, a lokacin da ake baje kolin kayayyakin tarihi na kasar a wannan birnin. Bayanin ya ci gaba da cewa kayyakin tarihin sun hada da wani kur'ani rubutun hannu da wani tsohon malami ya rubutu shekaru da dama da suka gabata, wanda kuma wannan kur'ani yana daya daga cikin abubuwan tarihi da aka adana a kasar. An yi wa bangon kur'anin ado da wasu ababe masu kyalli. Da dama daga cikin mahalarta taron dai sun nuna gamsuwarsu dangane da yadda aka adana kayan tarihi musamman ma wadanda suka danganci kur'ani a kasar, wadanda tarihinsu ke komawa zuwa ga daruruwan shekaru.

403094




captcha