Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Bahrain gna cewa; A cikin wata mai kamawa ne a karon farko za a gudanar da zaman taro na kasa da kasa domin yin bahasi kan batun saka hannayen jari a musulunce a birnin Qazan na jamhuriyar Tataristan. Rahoton ya ci gaba da cewa bankin musulunci ne ya dauki nauyin shirya gudanar da wannan zaman taron, domin kara karfafa gwiwar masu saka hannayen jari da ke sojn ganin mu'amalarsu da bankuna ta gudana ba tare da saba wa ka'idar musulunci a harkokin banki ba. Taron dai zai samu halarta masana daga cibiyoyin kudi da hadahadar kasuwanci da harkokin tattalin arziki daga sassa daban-daban na kasar Rasha, da kuma yankunan nahiyar turai gami da yankin gabas ta tsakiya, da kuma kudu da gabacin nahiyar Asia.
404511