IQNA

Wani jirgin Ruwa Na Swedeen Dauke Da Taimako Zai Kama Hanyar Gaza

14:54 - May 14, 2009
Lambar Labari: 1778317
Bangaren kasa da kasa: Babban masanin nan na kasar Swedeen Mathies Gardell ya bayyana cewa wannan taimako ne da aka tattara domin aikewa da shi zuwa ga al'ummar zirin Gaza da suke fuskantar matsananciyar wahala sakamakon ci gaba da killace su da Isra'ila ke yi, ya ce wanna jirgin ruwa zai kunshi wasu 'yan majalisa daga kasar Birtaniya da kuma kasar Swedeen.
Kmafanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Syria cewa; Babban masanin nan na kasar Swedeen Mathies Gardell ya bayyana cewa wannan taimako ne da aka tattara domin aikewa da shi zuwa ga al'ummar zirin Gaza da suke fuskantar matsananciyar wahala sakamakon ci gaba da killace su da Isra'ila ke yi, ya ce wanna jirgin ruwa zai kunshi wasu 'yan majalisa daga kasar Birtaniya da kuma kasar Swedeen. Rahoton ya ci gaba da cewa wannan makeken jirgin ruwa da zai tashi daga Swedeen zuwa Gaza yana dauke da muhimman abubuwan rayuwa da al'ummar yankin ke bukata, da hakan ya hada da kayayyakin abinci, magunguna, kayayyakin gine-gine, tsaftacr rowan sha da dai sauransu. Babbar manufar yin hakan ita ce karya takunkumin zalunci da Isra'ila ta kakaba wa yankin.

403962




captcha