IQNA

Kafofin Yada Labaran Larabawa Na Ci Gaba Da Yin Sharhi Kan Kalaman Jagora

23:48 - May 17, 2009
Lambar Labari: 1779590
Bangaren kasa da kasa: Jawabin da jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei a ziyzrzr da yake kaiwa lardin kurditan kan musulmi su yi hattara kan bangarorin da ke neman kawo rarraba tsakanin sunna da shi'a, hakan ya ja hankulan kafofin yada labaran kasashen larabawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Sharq alausat da ake bugawa a kasar Saudiyya cewa; Jawabin da jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei a ziyzrzr da yake kaiwa lardin kurditan kan musulmi su yi hattara kan bangarorin da ke neman kawo rarraba tsakanin sunna da shi'a, hakan ya ja hankulan kafofin yada labaran kasashen larabawa. Jaridar ta buga a wani shafinta da manyan bakake cewa; Ayatollah Khamenei ya bayyana cewa akwai wasu gungun jama'a da suke kokarin kawo rarraba ta mazhaba tsakanin al'ummar musulmi da sunan shi'a da sunna, ko sun sani ko ba su sani ba. Wasu daga cikin masu yin sharhi a cikin kasashen kan abubuwan da ke kai da komowa sun bayyana cewa, bayanan na jagora ba su rasa nasaba da wasu kalami na kafirta mabiya mazhabar shi'a da limamin masallacin Makka ya yi a makon da ya gabata.

405847


captcha