IQNA

Bangaren kasa da kasa: A jiya ne aka fara gudanar da taro kan hakkokin mata a addinin musulunci wanda cibiyar kula da harkokin mata ta kasar saudiyya ta dauki nauyin shirya a babban ginin cibiyar al'adu da harkokin musulunci da ke birnin Jiddah.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Aljazira da ake bugawa a kasar saudiyya cewa; A jiya ne aka fara gudanar da taro kan hakkokin mata a addinin musulunci wanda cibiyar kula da harkokin mata ta kasar saudiyya ta dauki nauyin shirya a babban ginin cibiyar al'adu da harkokin musulunci da ke birnin Jiddah. Babbar manufar gudanar da taron dai ita ce fayyace irin hakkokin da addinin musulunci ya bai wa mata, da kuma irin nauyin da ya rataya kansu wajen taka gagarumar rawa domin ci gaban al'umma a dukkanin sassa na rayuwa da tarbiya. Taron yana samun halartar manyan malamai dam asana daga kasashen daban-daban, inda suke gabatar da laccoci da kuma makalolinsu.

406329