IQNA

Kiristocin Iraki Sun Yi Allawadai Da Kafirta 'Yan Shi'a

16:33 - May 18, 2009
Lambar Labari: 1780040
Bnagaren kasa da kasa; Mabiya addinin kiristanci na kasar Iraki sun fitar da wani bayani a yau, da a cikinsa suka yi Allawadai da fatawar da wasu malaman wahabiyawa na kasar Saudiyya suka bayar a cikin 'yan kwanakin nan, da ke kafirta musulmi mabiya mazhabar shi'a tare da halasta jininsu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna yanakalto daga kamfanin dillancin Brana cewa; Mabiya addinin kiristanci na kasar Iraki sun fitar da wani bayani a yau, da a cikinsa suka yi Allawadai da fatawar da wasu malaman wahabiyawa na kasar Saudiyya suka bayar a cikin 'yan kwanakin nan, da ke kafirta musulmi mabiya mazhabar shi'a tare da halasta jininsu. Rahoton ya ci gaba da cewa daruruwan mabiya addinin kiristanci ne suka gudanar da wani gangami a kan manyan titunan garin Babul da ke kasar Iraki, domin nuna matukar kiyayyarsu da fatawar da malaman wahabiyawa na kasar saudiyya suka bayar kan kafirta shi'a da halasta jininsu, sun kuma yi kakkausar suka kan limamin masallacin makka wanda shi ne kan gaba wajen bayar da wannan fatawar, kamar yadda suka fitar da bayani da ke bayyana matsayinsu kan hakan.

406356


captcha