Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da taruka kan cika shekaru 61 da yahudawan sahyuniya suka mamaye yankunan palastinawa tare da kafa haramtacciyar kasar Isra'ila, tare da baje kayayyakin tarihi da suka dangancin kisan kiyashin da palastinawa suka fuskanta kafin kafa wannan haramtacciyar kasa ta yahudawan sahyuniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alqods cewa; Tun jiya ce aka fara gudanar da taruka kan cika shekaru 61 da yahudawan sahyuniya suka mamaye yankunan palastinawa tare da kafa haramtacciyar kasar Isra'ila, tare da baje kayayyakin tarihi da suka dangancin kisan kiyashin da palastinawa suka fuskanta kafin kafa wannan haramtacciyar kasa ta yahudawan sahyuniya. Rahoton ya ci gaba da cewa daga cikin muhimman kayayyakin da aka baje a jami'ar birnin Gaza hard a hotunan dubban shahidai wadanda suka bayar da jininsu domin kare martabar kasarsu da al'ummarsu da addininsu da kuma wurare masu tsarki da ke cikin palastinu. Haka nan kuma an nuna wasu hotunan dangane da halin da palastinawa masu gudun hijira suke ciki bayan da aka fitar da su daga yankunansu da gidajensu.
406391