IQNA

16:54 - May 20, 2009
Lambar Labari: 1781074
Bnagaren kasa da kasa: Sakataren cibiyar kula da harkokin addinin musulunci a Chechniya Solban Khasimov ya bayyana cewa a karon farko an samara da wata hanya ta koyar da makafi karatun kur'ani mai tsarki a Chechniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet Russia today cewa; Sakataren cibiyar kula da harkokin addinin musulunci a Chechniya Solban Khasimov ya bayyana cewa a karon farko an samara da wata hanya ta koyar da makafi karatun kur'ani mai tsarki a Chechniya. Ya ci gaba da cewa hukumar kula da harkokin addinin musulunci ta yankin ta dauki nauyin wasu mutane 12 tun sheakarun domin su tafi kasar Tataristan domin koyon hanyoyin da ake bi wajen koyar da makafi karatun kur'ani mai tsarki, kuma cikin ikon Allah sun kammala karatun nasu sun komo gida domin ci gaba da koyar da makafi karatun kur'ani mai tsarki.

407604
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: