IQNA

Murnar al'ummar Gaza a asibitin shahidan Al-Aqsa bayan isar makamai masu linzami na Iran

15:59 - April 14, 2024
Lambar Labari: 3490983
Falasdinawa da ke asibitin shahidan Al-Aqsa da ke Deir al-Balah a tsakiyar zirin Gaza sun yi murna tare da yin kabbara a daidai lokacin da makamai masu linzami na Iran suka isa yankunan Falastinawa da Isra’ila ta mamaye.

Murnar al'ummar Gaza a asibitin shahidan Al-Aqsa bayan isar makamai masu linzami na Iran

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, a safiyar yau Lahadi ne al’ummar Palastinawa na zirin Gaza suka gudanar da bukukuwan mayar da martani ga Iran dangane da harin da aka kai kan karamin ofishin jakadancin Iran da ke birnin Damascus.

Jajirtattun sojojin sama na dakarun kare juyin juya halin Musulunci a safiyar yau Lahadi, tare da sauran dakarun wannan kungiya mai fafutukar neman sauyi da farin jini, da zummar hukunta haramtacciyar kasar Isra'ila da muggan laifukanta, inda aka kaddamar da farmakin ramuwar gayya na "Alkawari na Gaskiya". Inda da dama daga cikin makamai masu linzami da jirage marasa matuka sun yi luguden wuta a cikin yankunan da aka mamaye tare da auna filin jirgin saman sojojin mamaya a Naghab.

 

 

4210271

 

captcha