Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Sharq al-ausat cewa; Ministan harkokin wajen kasar Birtaniya David Wright Miliband ya yi kira ga kasashen yammacin turai da su sake yin nazari kan tunaninsu na kuskure da rashin fahimta kan addinin musulunci, kuma ya kamata al'ummomin yammacin turai suka rika girmama mabiya addinin musulunci maimakon wulakanta su da cin zarafinsu. Ministan harkokin wajen kasar ta Birtaniya ya furta hakan ne jiya a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a sashen gudanar da nazari kan addinin musulunci a jami'ar Oxford da ke birnin London. Ya ce bai kamata al'ummomin yammacin taurai su kyamaci muslumi ba, domin kuwa akwai abubuwa da dama da suka hada su, da bai kamata a dauki karan tsana a dora kan musulmi ba.
409061