IQNA

15:36 - May 24, 2009
Lambar Labari: 1782432

Juyin Juya Halin Musulunci A Iran Ya Kawo Sabon Sauyi A Duniya

Bangaren siyasa: Shugaban kasar Iran Mahmud Ahamadinejad ya fadi yau a ziyarar da yake kaiwa yankin Khormshahr cewa; juyin juya halin musulunci a Iran ya kawo wani babban sauyi a aladu da siyasar duniya, kuma hakan ya wayar da kan al'ummomi dangane da sama ma kansu mafita matukar dai suka motsa.

Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na shugaban kasar Iran cewa; Shugaban kasar Iran Mahmud Ahamadinejad ya fadi yau a ziyarar da yake kaiwa yankin Khormshahr cewa; juyin juya halin musulunci a Iran ya kawo wani babban sauyi a aladu da siyasar duniya, kuma hakan ya wayar da kan al'ummomi dangane da sama ma kansu mafita matukar dai suka motsa. Ahmadinejad ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban dubban mutane da suka taru a babban masallacin garin Khoramshahr, wanda kuma wannan ziyara ta z one a daidai lokacin da al'ummar Iran suke gudanar da taruka na tunawa da kwato garin Khoramshahr daga hannun 'yan jam'iyar Ba'as da suka mamaye garin a lokacin kallafaffen yakin da Iran ta yi da gwamnatin Saddam Hossain, wanda ya samu cikakken goyon baya daga kasashen yammacin turai domin kawo karshen juyin juya halin musulunci a Iran.

409560
captcha