IQNA

17:13 - May 25, 2009
Lambar Labari: 1782635
Bangaren kasa da kasa: Kakakin kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas Fauzi Barhum ya yi Allawadai da kalaman pira ministan Isra'ila Benjamin Natanyaho dangane da makomar birnin Qods, inda ya bayyana kalaman da cewa kalamai ne wuce gona da iri da kuma neman tsokanan al'ummar palastinu da ma musulmi baki daya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait KUNA cewa; Kakakin kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas Fauzi Barhum ya yi Allawadai da kalaman pira ministan Isra'ila Benjamin Natanyaho dangane da makomar birnin Qods, inda ya bayyana kalaman da cewa kalamai ne wuce gona da iri da kuma neman tsokanan al'ummar palastinu da ma musulmi baki daya. Fauzi Barhum ya ce furucin na Natanyaho da ke cewa birnin Qods shi ne fadar mulkin Haramtacciyar Kasar Isra'ila kalami ne na wuce gona da iri, da ya kamata dukkanin mabiya addinai da aka safkar daga sama su yi Allawadai da shi, domin hakan na nuni ne da cewa sabuwar gwamnatin yahudawan sahyuniya na da kudirin tsananta ta'addanci kan al'ummar palastinu, tare da ci gaba da mamaye yankunan palastinawa da ke gabacin birnin Qods.

410071
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: