IQNA

Jami'ar Azhar Ta Haramta Wani Littafin Magunguna Da Aka Danganta Da Kur'ani

0:05 - May 29, 2009
Lambar Labari: 1784329
Bangaren kasa da kasa: Kwamitin kula da harkokin nazari da buge-bugen littafai na jami'ar Al-azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar, ya haramta wani littafi mai suna kur'ani domin yin magani, tare da hana buga shi ko sayar da shi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar akidati ta kasar Masar cewa; Kwamitin kula da harkokin nazari da buge-bugen littafai na jami'ar Al-azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar, ya haramta wani littafi mai suna kur'ani domin yin magani, tare da hana buga shi ko sayar da shi. Shugaban kwamitin sheikh Ali Abdulbaki ya bayyana cewa; wasu suna yin amfani da kur'ani wajen cimma burinsu na kasuwanci da neman kudi bisa abin da ba gaskiya ba ne, kuma babban abin ban takaicin shi ne yadda suke dangantaka irin wadannan ayyuka na sun a neman kudi da sunan yin magani ga jama'a da kur'ani, ya ce wannan ya saba wa shari'ar muslunci, a kan haka ne ma suka dauki mataki haramta wani littafi da aka buga bisa irin wannan manufa.

411952


captcha