Bangaren siyasa: Shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; daga cikin hikimomin Imam Khomeini shi ne hada addinin da siyasa, ba tare da an raba sub a, domin kowane dayansu yana tafiya tare da dayan kafada da kafada.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; daga cikin hikimomin Imam Khomeini shi ne hada addinin da siyasa, ba tare da an raba sub a, domin kowane dayansu yana tafiya tare da dayan kafada da kafada. Ali larijani ya bayyana hakan ne jiya a lokacin da wakilan majalisar shawara ta kasar Iran suka kai wata ziya a hubbaren Imam Khomeini domin jaddada mubaya'arsu gare shi da kuma tabbatar da cewa suna kan tafarkin juyin juya halin muslunci da ya jagoranci kafawa a Iran. Larijani ya ce daya cikin almajiran Imam Khomeini ya isa ya zama misali na sanin matsayin Imam, wato marigayi Ayatollah Ozma Muhammad Taki Bahjat, wanda daya daga cikin mutane da ake buga misali da su a duniya wajen tsaron Allah da gudun duniya, da mayar da al'amari baki daya ga Allah madaukakin sarki.
412276