Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait KUNA cewa; An fara gudanar da wani taro domin nuna cikakken goyon baya ga al'ummar palastinu marassa kariya a birnin Istanbul na kasar Turkiya. A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a gaban taron, shugaban gamayyar kungiyoyin musulmi na kasashen duniya Najmi Sadiq Auglo ya bayyana cewa; batun palastinu batu ne da ya shafi musulmi baki daya, kuma wajibi ne da ya rataya kan dukkanin musulmi da su safke nauyin da ya rataya kansu na taimakon 'yan uwansu da ke fuskantar zalunci daga yahudawan sahyuniya, kuma wajibi ne a kan dukkanin musulmi su kare wurare masu alfarma da ke birnin Qods.
413687