Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Masar cewa; Mataimakin babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa ya kirayi shugaban kasar Amurka Barack Obama, da ya yi mu'amala da addinin musulunci a matsayin addinin sulhu da zaman lafiya. Muhammad Sabih ya bayyana hakan ne yau a lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar, inda ya ce ya kamata Obama ya canja mahangar gwamnatin Amurka dangane da musulunci, musamman ma mahangar shugabannin gwamnatin da ta gabace shi, wadanda suka dauki siyasar karan tsana suka dora kan addinin musulunci. Ya ce ko shakka babu siyasar gwamnatin Amurka da ta gabata ta ginu kan kuskure, lamarin da ya jawo wa Amurka bakin jinni a fadin duniya, musamman ma a kasashen musulmi.
413817