Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Aswat Iraki cewa; An fara aiwatar da wani shiri na kasa da kasa na bayar da horo dangane da adana kayan tarihin musulunci a Iraki, wanda yanzu haka aka bayar da wannan horo garin Aur da ke cikin lardin Nasiriyya da ke arewacin kasar. Rahoton ya ci gaba da cewa babbar cibiyar kiyayewa tare da adana kayan tarihin musulunci tare da hadin gwiwa da bangaren kula da kayan tarihi na ma'aikatar al'adu ta kasar Italia, gami da hukumar kula da kananan yara ta Majalisar dinkin duniya, su ne suka shirya wannan bayar da horo kan adana kayan tarihin musulunci da ke kasar Iraki. Shugaban cibiyar kiyayye kayan tarihi na kasar Iraki Abdulamir Hamdani ya bayyana cewa; taron na samun masana daga sassa daban-daban na kasashen muslmi da na larabawa da ma nahiyar turai.
414464