Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran WAM cewa; an fara gudanar da wani zaman tattaunawa na kasa da kasa tsakanin addinai da aka safkar daga sama a birnin Kirwan na kasar Tunisia. Bayanin ya ci gaba da cewa taron wanda kungiyar kula da harkokin ilimi da al'adu na kasashen musulmi gami da hadin gwiwa tare da majalisar dinkin duniya, zai samu halartar masana sama da dari daya daga kasashen duniya sama da talatin, inda za su yi dubi kan muhimmman batutuwa da suka hada addinai, tare da bijiro da abubuwan da dukkanin addinan suka yi amanna da su, wanda ko shakka babu hakan zai taimaka wajen kara kusanto da fahimta a tsakaninsu.
415051