IQNA

'Yan Jam'iyar Labour Sun Amince Da Gina Makarantun Musulunci A Birtaniya

19:45 - June 05, 2009
Lambar Labari: 1786812
Bangaren kasa da kasa: 'Yan jam'iyar Labour sun amince da batun gina makarantun musulunci a fadin kasar Birtaniya, kuma sun sha alwashin za su bayar da dama ga musulmi domin ci gaba da yada manufofin addinin musulunci a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na islam online cewa; 'Yan jam'iyar Labour sun amince da batun gina makarantun musulunci a fadin kasar Birtaniya, kuma sun sha alwashin za su bayar da dama ga musulmi domin ci gaba da yada manufofin addinin musulunci a kasar. Rahoton ya ci gaba da cewa da dama daga cikin 'yan takara na jam'iyar Labour sun sha alwashin cewa matukar dai suka ci zabe za sub a musulmi dama da su gina makarantu a ko'ina suke so a cikin kasar domin koyar da ilimin addinisu cikin 'yanci ba tare da wata tsangwama ba. Da dama daga cikin mabiya addinin musulunci da ke zaune a kasar Birtaniya suna son saka 'ya'yansu makarantun addinin musulunci, amma suna fuskantar matsala saboda karancin makarantun.

414960


captcha