Bangaren kasa da kasa: A jiya ne kotun kasar Austarlia ta bayar da amsa dangane da hukuncinta kan batun gina wata makaranta ta musulunci, bayan dad a ki amincewa da hakan tun a cikin watan da ya gabata inda ta sake jadda kin amincewarta da hakan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na islam alyaum cewa; kotun kasar Austarlia ta bayar da amsa dangane da hukuncinta kan batun gina wata makaranta ta musulunci, bayan dad a ki amincewa da hakan tun a cikin watan da ya gabata inda ta sake jadda kin amincewarta da hakan. Bayanin ya ci gaba da cewa kotun ta fitar da hukuncin net un watan mayun da ya gabata, amma kwamitin kula da harkokin musulmi na kasar ya rubuta wata takarda zuwa ga kotun, inda ya bukaci da ta sake yin nazari kan wannan hukunci, domin bayar da dama ga musulmi su gina makarantar da zata dauki dalibai 900, amma a jiya kotun ta sake jadda hukuncinta na farko kan hakan.
415835