Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na gnne.nt cewa; Samir Jumail ya rubuta wani wasan kwaikwayo kan tarihin manzon Allah (SAW) wanda yanzu hakan an shirya shi zuwa kashi ashirin kuma da zaran an kammala shirye-shirye za a fara gudanar da shi a bainar jama'a. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan wasan kwaikwayo da aka rubuta za a aiwatar da shi a aikace a bainar jama'a a cikin fitowa daban-daban, kuma an kasa shi zuwa kashi ashirin da nufin bayyana tarihin manzon Allah (SAW) da kuma yadda ya fuskanci matsaloli wajen isar da sakonsa, gami da kyawan dabi'unsa da halayensa, wanda hakan ne ya ba shi babbar nasara wajen jan hankulan al'ummomin zuwa ga shiriyar day a zo ma dan adam da ita.
415781