Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Wam cewa; An fara gudanar da taro na ministocin harkokin kudi da tattalin arziki na kasashen musulmi a birnin Ishabad na kasar Turkmenestan, wanda zai kwashe tsawon kwanaki biyu ana gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa shugaban kasar Turkmenestan Kurban Muhaduv shi ne ya jagoranci bude zaman taron, wanda yak e yin dubi kan muhimman batutuwa da suka shafi harkokin kudi da tattalin arziki na kasashen musulmi. Yanzu haka dai masana kan harkokin kudi da tattalin arziki da manyan daraktoci na bankunan kasashen musulmi da cibiyoyin harkokin tattalin arziki da kasuwanci na kasashen musulmi sama da 600 ne daga kasashe 56 ke halartar wannan zaman taro.
415730