IQNA

An Kawo Karshen Gasar Karatun Kur'ani Ta Mata A Saudiyya

19:41 - June 05, 2009
Lambar Labari: 1787231
Bangaren kasa da kasa: An kawo karshen gasar karatu da hardar kur'ani mai girma da aka gudanar a birnin Riyad fadar mulkin kasar saudiyya, inda aka girmama wadanda suka samu nasar lashe gasar a dukkain bangarorin da aka gudanar da ita.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Riyad cewa; An kawo karshen gasar karatu da hardar kur'ani mai girma da aka gudanar a birnin Riyad fadar mulkin kasar saudiyya, inda aka girmama wadanda suka samu nasar lashe gasar a dukkain bangarorin da aka gudanar da ita. Shugaban kwamitin kula d aharkokin matasa da al'dunsu na kasar saudiyya Fahad Alyan ya bayyana cewa, dukkanin wadanda suka shiga gasar matasa ne, wasu daga cikinsu sun gudanar da gasar ne a bangaren hardar kur'ani, yayin da wasu kuma sun shiga bangaren karatu ne, kuma adadin matasan da suka shiga cikin gasar sun kai 854. Ya kara da cewa gudanar da wannan gasa na taimakawa matuka wajen jan hankula matasa zuwa ga karatu da hardar kur'ani mai tsarki.


415644
captcha