Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da taro karo na uku na kasa da kasa a zirin Gaza, domin nuna cikakken goyon baya ga Qods, da kuma kare masallacin da birnin mai alfarma daga dukkanin shishigin yahudawan sahyuniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na tashar talabijin din palastine cewa; An fara gudanar da taro karo na uku na kasa da kasa a zirin Gaza, domin nuna cikakken goyon baya ga Qods, da kuma kare masallacin da birnin mai alfarma daga dukkanin shishigin yahudawan sahyuniya. Daya daga cikin wadanda suka shirya gudanar da wannan taro Safi Khalid ya bayyana cewa; an fara gudanar da wannan taro ne domin kara tunatar da al'ummomin duniya dangane da halin da masallacin Qods mai alfarma yake ciki, da kuma barazanar da yake fuskanta daga yahudawan sahyuniya masu tsattsauran ra'ayi, yayin da kuma Isra'ila ke ci gaba da mamaye yankunan palastinawa da ke gabacin Qods.
417277