IQNA

Gwagwarmayar Musulmi Ce Ta Tilasta Wa Amurka Canja Siyasarta

17:18 - June 09, 2009
Lambar Labari: 1788999
Bangaren kasa da kasa; Jawaban da Shugaban kasar Amurka Barck Obama ya gabatar a birnin Alkahira na kasar Masar, hakan manuniya ce kan cewa gwagwarmayar al'ummar musulmi ce ta tilasta gwamnatin Amurka daukar matakan canja siyasarta, duk da cewa ba a ga abin da yake fada a aikace ba.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na saffar.org cewa; malamin nan na kasar Saudiyya kuma daya daga cikin jagororin mabiya mazhabar shi'a na kasar Saudiyya Sheikh Hassan Saffar ya bayyana cewa; Jawaban da Shugaban kasar Amurka Barck Obama ya gabatar a birnin Alkahira na kasar Masar, hakan manuniya ce kan cewa gwagwarmayar al'ummar musulmi ce ta tilasta gwamnatin Amurka daukar matakan canja siyasarta, duk da cewa ba a ga abin da yake fada a aikace ba. Ya ci gaba da cewa duk da cewa a cikin maganganun da Obama ya yi a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a birnin Alkahira ya fadi wasu abubuwa masu kyau, amma kuma dole ne Amurka ta canja siyasarta kan a bin da take kira yaki da ta'addanci.


417826
captcha