Bangaren manema labarai: ofishin da ke kula yada al'adun Iran a kasar serilanka tare da hadin guiwar Jami'o'in Kalaniya,Paradaniya sun fara wani taron nazarin rawar da musulunci ke takawa wajen samara da ci gaba>
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: bangaren hulda da jama'a a ofoshin da ke kula da yada al'adun kasar Iran a kasar serilanka tare da hadin guiwar wasu jami'o'in sun shirya wani taro da nazari kan yadda addinin musulunci ke taka rawar gani wajen ci gaban kasashe da al'ummomi .Wannan taro an shirya gudanar da shi ne a daidai lokacin da ake tunawa da ranar zagayowar ranar rasuwar mu'assasin juyin juya halin musulunci a Iran imam Khomeini ®.
416659