Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen kasar Labanan ya habarta cewa; An fitar da wani littafi mai suna salon karatun matanin kur'ani a zamanin yau a kasar Labanan, wanda cibiyar kula da harkokin yada al'adu da tunanin Musulunci da ci gabansa a kasar labanan. Bayanin ya ci gaba da cewa, babbar manufar littafin ita ce samar da wata hanya mafi sauki da za a iya yin amfani da ita wajen karanta matanin kur'ani mai tsarki, da ta yi daidai da zamanin da muke rayuwa a cikinsa. Bayanin ya ci gaba da cewa an yi amfani da salon rubutu mai kayatarwa wajen rubuta littafin, da kuma yadda yadda za a iya karanta kur'ani ta hanya mai sauki.
418046