IQNA

Al'ummar Japan Ba Su Amince Da Wulakanta Addinin Musulunci Ba

17:05 - June 10, 2009
Lambar Labari: 1789655
Bangaren kasa da kasa; Son zaman lafiya da ke cikin zukatan mutanen kasar Japan da kuma yin aiki da hankali cikin lamurra, shi ne ya sanya su ba su wulakanta addinin Musulunci, kuma ba su amince da duk wani matakin tozarta musulmi ko Musulunci ba, kuma suna kusanta kansu da musulmi tare da girmama wurare masu tsarki musulmi ke girmamawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar kasa da kasa Sharq ausat cewa; Shugaban cibiyar kula da harkokin addini da kuma tattaunawa tsakanin addinai Tayyib Mukhtar tya bayyana cewa; Son zaman lafiya da ke cikin zukatan mutanen kasar Japan da kuma yin aiki da hankali cikin lamurra, shi ne ya sanya su ba su wulakanta addinin Musulunci, kuma ba su amince da duk wani matakin tozarta musulmi ko Musulunci ba, kuma suna kusanta kansu da musulmi tare da girmama wurare masu tsarki musulmi ke girmamawa. Ya ci gaba da cewa matakin da al'ummar japan suke dauka da kuma abin da suka nuna a aikace dangane da addinin Musulunci abin yabawa ne, ya ce addnin Musulunci addini ne na marassa rinjaye a japan amma kuma suna samun girmama a daga al'ummar kasar.

418298





captcha