IQNA

17:05 - June 10, 2009
Lambar Labari: 1789658

A Karon Farko Wata Musulma Mai Hijabi Ta Shiga Majalisar Dokokin Belgeum

Bangaren kasa da kasa; A karon farko wata mace musulma mai saka hijabin musulunci ta lashe zaben majalisar dokokin kasar, inda za ta shiga majalisar a matsayin musulma kuma mai saka hijabin musulunci, kuma ita ce 'yar majalisa mafi karancin shekaru a tsakanin 'yan majalisar.

Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar alwatan cewa; A karon farko wata mace musulma mai saka hijabin musulunci ta lashe zaben majalisar dokokin kasar, inda za ta shiga majalisar a matsayin musulma kuma mai saka hijabin musulunci, kuma ita ce 'yar majalisa mafi karancin shekaru a tsakanin 'yan majalisar. Bayanin ya ci gaba da cewa matar mai suna mahanur 'yar asalin kasar Turkiya ce, amma tana rayuwa a kasar Belgeum, a cikin wata zantawa da ta hada da manema labarai a ta bayyana cewa; hijabi sutura ce ta addinin musulunci, kuma ita musulma ce, kuma saka hijabi bai yi karo da ko daya daga cikin dokokin kasar ba, akan hakan za ta saka hijabinta kuma ta shiga majalisar dokokin kasar domin wakiltar mutanen da suka zabe ta.


418370


captcha