Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar hadaddiyar daular larabawa wam cewa; Kwamitin kula da harkokin ilimi da al'adu na na musulmi mazauna kasashen da suke marassa rinjaye ya gudanar da zamansa a birnin Ribat na kasar Morocco, inda ya tattauna muhimman batutuwa da suka shafi halin da musulmi suke ciki a irin wadanan kasashe, da kuma hanyoyin da za a bi a karfafa musu gwiwa. Bayanin ya ci gaba da cewa taron ya samu halartar babban sakataren kwamitin Abdulaziz bin Usman Al-tuwaijari, wanda ya gabatar da jawabi yana mai cewa; kwamitin yana da wani shiri na musamman domin agaza wa musulmi marassa rinjaye da ke zaune a wasu kasashen ketare, ta yadda za su ci gaba da gudanar da harkokinsu na addini kamar yadda ya kamata.
418812