IQNA

23:48 - July 07, 2009
Lambar Labari: 1799300

Duk Da Sabanin Ra'ayi Na Siyasa Al'ummar Iran Suna Da Hadin Kai Wajen Tunkarar Makiya

Bangaren siyasa; Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya ja kunnen kasashen duniya masu girman kai dangane da shigar shigular da suke cikin harkokin Iran na cikin gida.

Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na ofishin jagoran juyin juya halin musulunci cewa; A jiya ne jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya ja kunnen kasashen yammacin turai dangane da shigar shugular da suke yi a cikin harkokin Iran na cikin gida. Ayatollah Khamenei ya yi wannan jan kunnen ne kuwa a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron maulidin Imam Ali (AS) da aka gudanar a Tehran. Ya ce makiya Iran su kwana da sanin cewa abin da ya faru a 'yan lokutan baya sabani na siyasa tsakanin 'yan takara da magoya bayansu, amma ba sabani ne kan tsarin musulunci a Iran ba kamar yadda wasu bangarori ke ta hankoron bayyanawa, wanda kuma wasu daga cikin gwamnatocin kasashen yammacin turai sun yi zaton za su iya yin amfani da wannan dammar wajen hargitsa lamurra a Iran da nufin kawo karshen tsarin musulunci, wanda hakan ke kara tabbatar da jahilcinsu kan tsarin da kuma akidar da ya ginu a kanta.Ya kara da cewa, ya zama wajibi a kan shugabanin kasashe masu girman kai su kwana da sanin cewa, ba za su iya yin fani da sabanin siyasa wajen yin shigar shugula a cikin harkokin Iran na cikin gida ba, domin kuwa shigarsu cikin harkokin Iran na cikin gida shi ne zai kara hada kan al'ummar Iran tare da mantawa da duk wani sabanin siyasa a tsakaninsu.Ya ce fitowar da Iraniyawa suka yi da kashi 85% wajen kada kuri'unsu, ya isa dalili da ke tabbatar wa wadannan kasashen da ma duniya cewa akwai 'yancin siyasa da demokradiyya a kasar, sabanin yadda makiyan Iran din suke ta kokarin bayyana wa duniya. Ayatollah Khamenei ya jaddada cewa da sannu za su yi dubi a kan dukkanin matakan da irin wadannan kasashe suka dauka na yin shigar shugula a cikin harkokin Iran na cikin gida, a lokacin gudanar da zabe da ma bayan kamala zaben, kuma ko shakka babu hakan zai bar mummunan tasiri a dangantakar da ke akwai tsakaninsu a nan gaba. Furucin na jagoran juyin juya halin musulunci a Iran na dauke ne da muhimmin sako ga kasashen yammacin turai, wadanda suka nuna rashin jin dadinsu karara bayan da shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinejad ya sake lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a Iran, wanda suke kallonsa a matsayi mai tsattsauran ra'ayi wajen kiyaye tsarin musulunci da kasar ke tafiya a kansa, ba'ada bayan haka kuma shugaba Ahmadinejad kurarsa ta yi kuka wajen nuna kiyayyarsa a fili dangane da zaluncin da Haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi kan al'ummar palastinu marassa kariya. Irin yadda kasashen yammacin turai suka yi amfani da sabanin siyasar da aka samu tsakanin 'yan takarar neman shugabancin kasa a Iran wajen tsoma baki cikin harkokin Iran na cikin gida, ya sanya Iran din daukar matakai na nuna ba sani ba sabo wajen taka musu birki, tare da shan alwashin sake yin nazari dangane da makomar alakarsu a zamuna masu zuwa, lamarin da ya tilasta wa wasu daga cikin irin wadannan kasashe nade tabarmar kunya da hauka.
430342

captcha