IQNA

An Saka Wani Tsohon Kur'ani A Cikin Dadaddun Littafai Na Tarihi A China

23:26 - July 10, 2009
Lambar Labari: 1799719
Bangaren kasa da kasa; An saka wani dadadden kur'ani da aka rubuta da ahhnu a cikin dadaddun littafan tarihi na kasar china guda goma sha biyu, wanda tarihinsa yake komawa zuwa ga shekaru 700 da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na almanar cewa; An saka wani dadadden kur'ani da aka rubuta da ahhnu a cikin dadaddun littafan tarihi na kasar china guda goma sha biyu, wanda tarihinsa yake komawa zuwa ga shekaru 700 da suka gabata. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan kur'ani na daya daga cikin muhimman littafai da ake la'akari da su a matsayin dadadun littafai da aka wallafa a kasar na tsawon shekaru, wanda tarihinsa yak e komawa zuwa ga shekaru sama da 700 da suka gabata da samunsa a kasar, wanda kuma ake sa ran an rubuta kur'anin sama da shekaru 1000 da suka gabata ne. An samu wannan kur'ani a hannun kabilar salar, wadanda suke cikin kabilun musulmi na kasar china, kuma suna alfahari da wannan kur'ani a mtsayi littafinsu.

430943



captcha