IQNA

An Bude Cibiyar Al'adu Ta Kungiyar ISESCO Guenea Konakri

23:48 - July 12, 2009
Lambar Labari: 1800961
Bangaren kasa da kasa; An bude wata cibiyar al'adu ta kungiyar kula da harkokin ilimi da al'adun kasashen musulmi ISESCO a kasar Guenea Konakri a birnin Labe.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na islam online cewa; a ci gaba da kokarin da ake yin a bunkasa ilmomin addinin musulunci da al'adunsa a kasashen Afirka da ma sauran kasashen duniya da suka hada da na nahiyar turai, an bude wata cibiyar al'adu ta kungiyar kula da harkokin ilimi da al'adun kasashen musulmi ISESCO a kasar Guenea Konakri a birnin Labe. Wannan shiri na kasa da kasa ana gudanar da shi ne tare da hadin gwiwa tsakanin bangaren kungiyar ta ISESCO da kuma ma'aikatar kula da harkokin ilimi ta kasar. Kungiyar ta sha alwashin samar da dukkanin kayan da ake bukata domin gudanar da wannan aiki a kasar, da nufin yada al'adun addinin musulunci da kuma ilminsa a tsakanin al'ummar kasar.

431818


captcha