Bangaren kasa da kasa; Musulmin kasar amurka sun bayyana cewa ba za su halarci taron marubutan kasar ba, wanda cibiyar kula da dakunan karatu ta kasar ta shirya gudanarwa, saboda halartar da marubucin nan na kasar mai tsananin gaba da addinin musulunci zai yi a wajen taron.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na islam online cewa; Musulmin kasar amurka sun bayyana cewa ba za su halarci taron marubutan kasar ba, wanda cibiyar kula da dakunan karatu ta kasar ta shirya gudanarwa, saboda halartar da marubucin nan na kasar mai tsananin gaba da addinin musulunci zai yi a wajen taron. Bayanin ya ci gaba da cewa an fara gudanar da wannan taro a yau a birnin Chikago na kasar, wanda aka shirya kan cewa sama da wakilan kungiyoyi da cibiyoyin musulmi 50 ne za su halarci zaman taro, kamar yadda taron zai samu halartar marubuta daga sassa daban-daban na kasar, dukkanin kungiyoyin musulmin da aka gayyata dai bakinsu ya zo daya kan cewa ba za su halarci zaman taron ba, saboda gayyatar Robert Spencer da aka yi, wanda kuma shi mutum ne da ya shahara wajen kiyayya da musulunci.
432516