IQNA

Majalisar Musulmin Nahiyar Turai Ba Gamsu Da Fatawar Jinkirata Haji Ba

17:46 - July 13, 2009
Lambar Labari: 1801426
Bangaren kasa da kasa; Majalisar musulmin nahiyar turai ta sanar cewa ba ta amince da fatawar da wasu malamai a wasu kasashen larabawa suka fitar ba, da ke cewa za a iya jinkirta lokutan gudanar da ayyukan haji da Umra sakamakon yaduwar ciwon nan na murar aladu, wanda suke tsoron ka da ya yadu tsakanin musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na almuslim cewa; Majalisar musulmin nahiyar turai ta sanar cewa ba ta amince da fatawar da wasu malamai a wasu kasashen larabawa suka fitar ba, da ke cewa za a iya jinkirta lokutan gudanar da ayyukan haji da Umra sakamakon yaduwar ciwon nan na murar aladu, wanda suke tsoron ka da ya yadu tsakanin musulmi. Bayanin ya ci gaba da cewa dalilan da wasu malamai suka gabatar wanda hakan ne suka dogara da su wajen bayar da fatawa da ke neman daga lokacin gudanar da ayyukan haji, bayanin ya ce wannan fatawa da aka ftar tana tattare da gagarumin hadari. Bayanin ya ce abin da ya kamata shi ne a mayar da hankali wajen shawo kan matsalar.

432467




captcha