IQNA

An Bude Wani Taro Kan Qods Birnin Al'adun Larabawa

17:45 - July 13, 2009
Lambar Labari: 1801429
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wani taro kan Qods birnin ala'dun larabawa, wanda aka yi wa take da aminci ya tabbata ga Qods, wanda ma'aikatar kula da harkokin al'adu ta kasar Syria ta shirya gudanarwa a birnin Lazikiya na na kasar Syria.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sana na kasar yria cewa; An fara gudanar da wani taro kan Qods birnin ala'dun larabawa, wanda aka yi wa take da aminci ya tabbata ga Qods, wanda ma'aikatar kula da harkokin al'adu ta kasar Syria ta shirya gudanarwa a birnin Lazikiya na na kasar Syria. Bayanin ya ci gaba da cewa An fara gudanar da zaman taron net un ranar Asabar da ta gabata, taron yana samun halartar masana kan harkokin sadarwa da yada labarai daga kasashen larabawa daban-daban, inda suke yin bahasi dangane da irin rawar da dukkanin kafofin yada labarai na kasashen larabawa na yankin gabas ta tsakiya na arewacin Afirka za su iya takawa wajen kare martabar birnin Qods da kuma masallaci mai alfarma.

432450


captcha