Bangaren kasa da kasa; Kashe musulma 'yar kasar Masar da aka yi a kasar jamus a cikin kotu, da kuma yadda 'yan sanda kasar suka ki yarda a gudanar da bincike kan hakan, na nuni da hakikanin siyasar kasashen turai dangane da addinin musulunci da musulmi.
Kmafanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na cibiyar kula da harkokin mazhabar iyalan gidan manzon Allah cewa; Kashe musulma 'yar kasar Masar da aka yi a kasar jamus a cikin kotu, da kuma yadda 'yan sanda kasar suka ki yarda a gudanar da bincike kan hakan, na nuni da hakikanin siyasar kasashen turai dangane da addinin musulunci da musulmi, kuma hakan zai kara tunzuwa masu tsananin gaba da addinin musulunci a nahiyar turai da Amurka ta arewa awajen ci gaba da nuna kyama ga mabiya addinin musulunci. Bayanin ya ci gaba da cewa dole ne kasashen musulmi su dauki mataki na bai daya wajen fuskantar wannan mummunar siyasa ta kasashen turai a kan musulmi.
433034