IQNA

Za A Kafa Wata Cibiyar Musulunci Mai Suna Marwah Sharbini A Jamus

15:42 - July 15, 2009
Lambar Labari: 1802502
Bangaren kasa da kasa; Kungiyoyin musulmi a kasar jamus gami da wasu daga cikin kawayen Marwah Sharbini, sun kudiri aniyar bude wata cibiyar harkokin musulunci tare da nazarin addini a birnin Sidn da ke gabacin kasar jamus da za a saka wa Suna Marwa Sharbini.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Nasij cewa; Kungiyoyin musulmi a kasar jamus gami da wasu daga cikin kawayen Marwah Sharbini, sun kudiri aniyar bude wata cibiyar harkokin musulunci tare da nazarin addini a birnin Sidn da ke gabacin kasar jamus da za a saka wa Suna Marwa Sharbini. Bayanin ya ci gaba da cewa tun kafin rasuwar marwa akwai shirin gina wannan cibiya, amma bayan abin day a faru da ita sakamakon saka hijabin musulunci wadanda suke kul ada shirin gina wannan cibiya sun yanke shawara kan a saka wa cibiyar sunan Marwa Sharbini, domin girmama ta. Bayanin ya ci gaba da cewa ko da ma an saku saku da batun gina cibiyar, amma abin da ya faru da marwa ya kara tayar da batun.

433744





captcha