IQNA

15:42 - July 15, 2009
Lambar Labari: 1802503

An Fara Gudanar Da Taron Tattaunawa Tsakanin Addinai A Austaria

Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da zaman tattaunawa na kasa da kasa tsakanin mabiya addinai daban-daban a birnin Vienna fadar mulkin kasar Austaria, wanda yake samun halartar masana da kuma malaman addinai daban-daban.

Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar shar al-ausat cewa; An fara gudanar da zaman tattaunawa na kasa da kasa tsakanin mabiya addinai daban-daban a birnin Vienna fadar mulkin kasar Austaria, wanda yake samun halartar masana da kuma malaman addinai daban-daban. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro nana gudanar da shi ne a matsayin ci gaba da taron nan da aka fara gudanarwa a birnin Washington da kuma Madrid, wanda sarkin kasar saudiyya Abdullah Bin Abdulaziz ya bayar da shawarar gudanar da shi. A lokacin bude zaman taron Abdullah bin Muhsin Al-turaiki ya bayyana cewa, babbar manufar gudanar da taron dai ita ce samun fahimtar juna tsakanin mabiya addinai, da kuma yi wa kowane daya bangare adalci maimakon kyamar juna.

433767

captcha